Ƴan Nijeriya miliyan 1.2 sun ci gajiyar Naira biliyan 66 na asusun ceto na MSMEs — Gwamnati

A ranar Talata ne gwamnatin tarayya ta ce ta raba Naira biliyan 66 ga ƴan Nijeriya miliyan 1.2 a karkashin shirin asusun ceto na tallafa wa masu kananan sana’o’i, MSMEs.

Ƙaramar Ministan Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari, Ambasada Mariam Katagum ce ta bayyana haka a wajen wani taro da aka yi a babban birnin tarayya Abuja na wadanda suka ci gajiyar asusun na MSME da kuma sauran tallafi a Abuja.

A cewar ministar, shirin a karkashin shirin dorewar tattalin arzikin Najeriya, NESP, ya raba kudaden kai tsaye ga wadanda suka ci gajiyar shirin.

Maƙasudin taron shi ne bayyana nasarorin da shirin ya samu a kasar da kuma karbar ra’ayoyin masu cin gajiyar shirye-shiryen tallafin gwamnati.

Tarurukan da suka gudana a lokaci guda a Legas, Kano, Bauchi, Enugu da kuma Edo, sun kuma kasance wata kafar wayar da kan jama’a kan shirye-shiryen da kuma sanin hanyoyin cin gajiyar su.

Katagum ta ce an dauki wannan tsarin ne saboda bukatar gyaran tattalin arzikin kasar bayan kullen korona, musamman ga kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa da masu sana’o’in dogaro da kai da a baya suke samu a sana’o’in da suke yi.

News All.