Wani matasi ya karɓi musulunci a hannun Sheikh Ahmad Sukairaj Dutsin-ma. 

“Wani bawan Allah ya karɓi musulunci a garin Dutsinma a ranar Alhamis din data gabata.”

“Wani bawan Allah ya karbi addinin islama a hannun Alshaik Ahmad sukairaj shugaban fityanul Islam ta jahar Katsina kuma babban Limamin masallacin juma’a na ƙofa a garin Dutsinma, Bayan da babban malamin ya ratafa masa Kalmar shahada daga ƙarshe ya buƙaci asaka masa suna Muhammad.”

“Ansaka masa suna Muhammad kuma aranar juma’ar data gaba ta sun sallaci sallar juma’a tare babban malamin addinin wanda shine babban limamin masallacin na ƙofa dake a garin Dutsinma ɗin.”

 

“Taruruwar musulmai ne suka tayashi murnar da kuma yi Mashi fatan Alkhairi na samun ni’imar musulunci kuma daga ƙarshe malamin yayi masa addu’oi da kuma riƙo da kyakkyawan ayyuka domin koyi damai sunan da aka saka Mashi.”