Innnalillahi wa inna ilaiyi rajiun magidanci ya kashe matarsa don ta shanye masa koko
Wani matashi mai shekaru 20 ya halaka matarsa bisa rikicin da suka samu sabida Koko kamar yadda majiyoyi suka tabbatar, kamar yadda shafin “Labarun Hausa” suka ruwaito.
An samu labarin yadda lamarin ya faru a kauyen Kadaura dake Karamar hukumar “Rafi”, inda matar ta rasa ranta bayan mijinta ya zane ta.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar “DSP Wasiu Abiodun” ya bayyana cewa:
Wanda ake zargi ya riga ya amsa laifinsa inda yace, karamin sabani suka samu tsakaninsa da matarsa sabida koko wanda hakan yasa ya dake ta.
Take anan ta fadi rashe-rashe wanda aka zarce da ita asibitin Wushishi rai ahannun Allah daga nan likitoci suka tabbatar ta rasu.
Kakakin rundunar ‘yan sanda ya bayyanawa manema labarai cewa, yanzu haka matashin yana hannun ‘yan sanda a babban ofishinsu dake Kagara yana amsa tambayoyi.
A cewar Abiodun, bincike ya kammala kuma za’a gurfanar da wanda ake zargin a gabankotu.
Rahoto daga shafin
