Adam A Zango Yana Neman Addu’ar Masoyan Sa Yarsa Daya Tilo Tana Can Kwance Asibiti Rai A Hannun Allah

Adam A Zango Yana Neman Addu’ar Masoyan Sa Yarsa Daya Tilo Tana Can Kwance Asibiti Rai A Hannun Allah

 

To Allah Ya Bata Lafiya.

 

 

 

A Wani Labarin Kuma Na Daban Ga Jarumin Wanda Ta Faru Akwanakin Baya.

 

 

 

Waiwaye Akan Labarin Ummi Rahab

 

ABINDA YA RABA TSAKANINSU BA MAI KYAU BANE

 

 

 

Ance mahaifiyar Ummi Rahab itace ta damka amanar ‘yarta wa Adam Zango tun tana yarinya karama bata balaga ba

 

 

 

Kuma Adam Zango ya sakata a fina-finai har duniya ta santa, Ummi Rahab tana hannun Adam Zango har zuwa yanzu da ta balaga ta tumbatsa tana ganin ta kai

 

Gargadin Naziru Sarkin Waka Ga Masu Zagi

 

 

 

Mahaifiyar Ummi Rahab ta rasu watanni kadan da suka wuce, sai gashi yanzu an wayi gari Adam Zango ya sallami Ummi Rahab, ita kuma tana masa gargadi da ya dena mata batanci imba haka ba zata tona masa asiri

 

 

 

Kamar yadda aka saba Datti Assalafiy ya gudanar da bincike, kuma na samu tabbacin cewa tabbas Adam Zango ya rabu da Rahab, kuma rabuwar banza sukayi, rabuwar uwaka ubanka, na kuma samu bayani akan abinda ya rabasu har ita Rahab tayi barazanan tona masa asiri bayan BBC Hausa sunyi hira da Adam Zango a jiya Alhamis inda ya fadi wata kalma

 

 

 

Na fahimci cewa hakika mahaifiyar Ummi Rahab (Allah Ya jikanta) tayi babban kuskure da ta dauki amanar ‘yarta ta damkashi a hannun wanda shima yana bukatar a bashi tarbiyyah

 

 

 

Gaskiya wannan rayuwa rikon amana tayi karanci, cin amana ya yawaita, ba kowa ake bawa amana ba, wadanda ake ganin suna da tsoron Allah a wannan zamanin suna iya cin amana, balle ‘yan daudu masu lalata tarbiyyan al’ummah

 

 

 

Malaman tarbiyya Islama sunce, ko halal ce akwai wata halal din da ana barinta don kunya, balle abinda bai halalta ba

 

 

 

Shawaran da zan bamu shine:

 

Duk wanda Allah Ya bashi mata da ‘ya’ya musamman mata, to yayi kokarin basu tarbiyya ta addini, a wannan zamanin ba’a bada amanar mata, walau matarka na aure ko ‘yarka da ka haifa, idan suka samu tarbiyya da juriya suna sana’a ko mutuwa kayi zasu kubuta da taimakon Allah

 

 

 

Allah Ka tsare al’ummar Musulmin Kasar Hausa daga sharrin ‘yan Hausa film Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *