Tun a satin daya gabata ne muka baku labarin Auren jarumar Kannywood Halima Atete da za’a gudanar,Wanda za’ayi shagulgula iri daban-daban za kuma a daura Auren a ranar Asabar idan Allah ya kaimu.

Sai dai kuma duba da yanayin shaharar jarumar da kuma kabilar ta da kuma inda ta fito an fara shagalin bikin ne a ranar Laraba wanda zai kai har izuwa ranar daurin Auren ana damawa.

Sai dai majiyar mu bata gano jarumin Kannywood ko daya ba a wajen illa wanda yake aikin sautin gurin mai kamfanin Gidan Biki wato Sharukhan.

Ba tare da bata lokaci ba zaku iya kallon cikakken bidiyon shagalin bikin Halima Atete din anan kasa,kuci gaba da kasancewa damu domin samun labarai na abunda za’ayi a bikin nan gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *