Tsohuwa mai shekara tamanin da daya ta sauke alkurani

Dattijuwa mai suna Hajiya Asma’u Jibril wacce daliba ce a makarantar Hajiya Baraka Islamiyya Bachirawa a karamar hukumar Ungogo da ke jihar Kano, ta kasance daya daga cikin daliban makarantar sha biyu da suka yi saukar Kur’ani a karshen makon nan.
A hirarta da wakilin mu, Hajiya Asma’u ta bayyana kadan daga cikin abubuwan da suka taimaka mata wajen samun wannan nasara ta sauke Al’Kur’ani mai girma.

Acewar Dattijuwar, tun tana karama ta taso da sha’awar ta samu ilimi, kasancewar mahaifinta Malami ne, wannan ya sa ta ju tana da sha’awar ta gaje shi mahaifin na ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *