Wani mutum ɗan ƙasar Kamaru a cikin wani bidiyo da ya karaɗe shafin TikTok, ya nuna cewa gwamnatin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari tafi nesa ba kusa ba gwamnatin Paul Biya, shugaban ƙasar Kamaru.
Mutumin wanda yake magana cikin fushi a bidiyon, inda yake cewa mutanen ƙasar Kamaru sun rayu da wannan gwamnatin wacce bata taɓuka komai har na shekara 40. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
Yana jin haushi idan yaji ƴan Najeriya na ƙorafi
Yace a duk lokacin da yaji ƴan Najeriya na ƙorafi, ya kan ji hakan a matsayin wani shirme a cikin kunnen sa, tunda suna cikin yanayi mai kyau fiye da ƴan ƙasar sa.
Shugaban ƙasa Paul Biya na ƙasar Kamaru, ya kasance a kan karagar mulki tun shekarar 1982, hakan ya sanya ya kasance ɗaya daga cikin shugabannin da suka daɗe akan karagar mulki a nahiyar Afrika.
Mutane sun tofa albarkacin bakin su
Bori ya rubuta:
Shugaban ƙasar Equatorial Guinea shekarar sa 43, kuma har yanzu yana kan mulki.
@Nkirukamma Cherie Agusiobo ya rubuta:
Ɗan’uwa!!!! A matsayina na ɗan Najeriya mun tausaya muku. Tabɗi shekara 40!!! Ku sarki gare ku ba shugaban ƙasa ba.
@user2332734943352 ya rubuta:
Najeriya shekara 8 ne kawai amma har jini na ya dai na yawo a jikina.
@Asamaowei Molly ya rubuta:
Da ace muna da irin wannan shugaban ƙasa wanda yayi shekara 40, da mun yi kisa da yawa.
Ban taɓa ganin lusarin shugaban ƙasa irin Buhari ba -Salihu Tanko Yakasai

Leave a Reply