A karon farko, an kira sallar Juma’a a masallacin Germany

An samu damar yin kiran sallar juma’a a karon farko a wani babban masallaci a ƙasar Jamus, bayan share shekaru ana gwabzawa da hukumomin ƙasar.

Ana sa ran mutane 100,000 su halarci sallar juma’ar

Ladan ya samu damar rangaɗa kiran sallah a babban masallacin birnin Cologne da ke ƙasar Jamus da misalin karfe uku na ranar juma’ar nan da muke ciki. Aƙalla mutane 100,000 ake sa ran sun halarci sallar juma’a a masallacin kamar yadda Aljazeera ta wallafa.

Akwai wasu masallatai da aka basu damar aiwatar da kiran sallar juma’a a cikin su tuntuni, amma wannan yafi jan hankali saboda girma da kuma matsayin masallacin.

Birnin shine na huɗu a ƙasar ta Jamus

Tun a bara ne dai mahukuntan ƙasar ta Jamus suka baiwa masallatai a birnin Cologne, birni na huɗu a ƙasar damar gudanar da kiran sallar juma’a amma bisa sharaɗin cewa bazai wuce na tsawon mintuna biyar ba. Sannan kuma an sanya sharaɗin cewa ayi amfani da matsaikacin sauti a yayin kiran sallar.

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyib Erdogan ne dai ya ƙaddamar da masallacin a shekarar 2018. ‘Yan ƙasar ta Turkiyya ne dai ke gudanar da lamurran masallacin.

An ƙawata masallacin sosai da kayan ado na zamani. Masallacin dai yana a yankin Ehrenfeld, a tsakiyar birnin Cologne. Yana ɗauke da hasumiyoyi guda biyu. Haka nan cikin masallacin zai iya ɗaukar aƙalla mutane 1,200 don gudanar da ibadah.

‘Yan Turkiyya ne ke gudanar da masallacin

Wata ƙungiya ta ‘yan ƙasar ta Turkiyya mai suna DITIB ce ke gudanar da harkokin masallacin. Ƙungiyar ta bayyana cewa an samu yarjejeniya tsakanin su da hukumomin birnin kan kiran sallah da lasifika na tsawon shekara biyu. Hakan zai zama

matsayin gwaji ne don ganin yadda abun zai kaya.

“Munyi matuƙar murna sosai. Bari da akayi a kira sallah zai sanya musulmi suji kamar suna a gidaje.” inji Abdurrahman Atasoy, sakataren ƙungiyar ta DITIB.

Magajin garin birnin na Cologne ne dai ya bada damar barin musulmi su gudanar da kiran sallar juma’a, inda ya bayyana cewa suna maraba da kowa a birnin nasu.