A yau Ne Kotu Zata Yankewa Sheik Abduljabbar Hukunci wane fata kuke?

Mai Sharia Ibrahim sarki yola na Babbar kotun shari’ar musulunci dake kofar Kudu ne zai jagoranci yanke hukuncin.

Dama tunda farko , an saka Alhamis 15 ga Disambar da muke ciki domin yanke hukuncin kan shari’ar da ake yiwa Sheik Abduljabbar Nasir kabara bisa zarginsa da yin kalaman batanci ga fiyayyen halitta annabi Muhammad Sallallahu alaihi wasalam.

Malamin dai yasha musanta zargin da ake masa, tare Kuma da zargin lauyoyin da suke kare shi a lokuta da dama.