Abin Alajabi: Matar Da Ta Haifi Yan Tara Ta Dawo Gida Abinda Ba’a Taba Samu Ba
Ma’auranta ‘yan kasar Mali, Halima Cissé da mijinta Kader Arby, sun aje tarihin da ba’a taba yi a duniya ba.
Jariran Halima Cissé sun karya kundin tarihin duniya na Guinness na mafi yawan yaran da aka haifa a cikin haihuwa guda wanda suka rayu.
Yan matan biyar da maza hudu an haife su ne ta hanyar yiwa mahaifiyar tasu tiyata kuma daga karshe sun koma Mali, kasarsu ta haihuwa.
Mali: 4 ga Mayu, 2021, za ta kasance har abada a cikin zukatan wasu ma’aurata ‘yan Mali waɗanda suka dau hankalin duniya bayan haihuwar jariransu tara a lokaci ɗaya.
Uwa ta ja hankalin duniya
Duk ba burin Halima Cissé da mijinta Kader Arby su dau hanakalin duniya saboda yadda ba ya cikin tsarinsu, amma ya zasu yi tunda suna tare da sojojin kasar mali.
Babu shakka haihuwa ce ta musamman yayin da aka haifi jarirai tara ta hanyar tiyata kuma wacce ta kasance cikin sauri. Rahotan legit.ng.
Ta Haihu a Maroko
Lokacin da aka ga halin da take ciki, kuma likitocin Mali basu iya ba, sai suka kwantar mata da hankali sannan suka kaita kasar Maroko dominta samu kulawa ita da ‘ya’yanta
Leave a Reply