Acuci mata: Amarya ta fasa aure ana tsaka da shagali bayan gano angonta na da sanko

Wani labari mai cike da ban mamaki ya bayyana wani wata amarya ta shafa wa idanunta toka ta fasa auren angonta bayan ta gano cewa yana da sanko, Amihad.com ta ruwaito.

Bayan kwashe lokaci mai tsawo ana shirye-shiryen aure a kasar Indiya, amaryar ta kalli cewa ba za ta iya jure ganin kan angonta da sanko ba yasa ta fasa auren.

Dama idan aure ya matso, dayawa ana samun matsaloli, ko dai daga bangaren ango ko kuma amarya. Wani lokacin kuma daga duk bangarorin.

Lamarin ya faru ne gundumar Etawah da ke birnin Kanpur cikin Jihar Uttar Pradesh, wanda sankon ango ya zama sanadiyyar fasa auren.

Jaridar Times of India ta bayyana yadda hankali kwance ake tsare-tsaren yadda za a gudanar da bikin har ta kai ga ma’auratan sun yi musayar furanni.

An samu tangarda ne bayan amaryar ta kula da cewa angon ya yi nadin gargajiya akansa ne musamman don ya boye sankon da ke kansa.

Take a wurin ta bukaci wasu daga cikin tawagarta da su taimaka su bincika mata gaskiya idan sumar bogi ce a kansa ko kuma ta gaskiya.

Bayan gaskiya ta bayyana, amaryar ta shiga tashin hankali mara misaltuwa. Ta tambayi angon dakanta don sanin gaskiyar lamarin, amma ya bayyana mata cewa dagaske sanko ne akansa.

Take anan ta fadi ta suma. Bayan dawowa daga hayyacinta, amaryar ta tsere inda ta ki amincewa a ci gaba da shagalin biki tare da ita.

Ta sanar da danginta cewa ba ta son auren mai sanko, kuma angonta yana da shi, ta fasa aurensa.

Babu yadda ba a yi da ita ba, amma ta murje idonta ta ce ba za ta taba yarda ta zauna da mai sanko ba. Danginta sun yi kokarin lallashinta amma abin ya ci tura.

Nan da nan magana ta karade ko ina, dangin mijin su ka dinga cece-kuce inda har wasu ke kallon kamar dama can yaudararsa ta yi.

Dattawan kauyen sun shiga lamarin inda su ka sasanta ta hanyar rarrashin dangin ango akan su hakura, nan da nan kowa ya watse.

Kamar yadda rahoton ‘yan sanda ya bayyana, duk bangarori biyun sun kai korafin junayensu yayin da dangin amaryar ke cewa an yaudare su ta hanyar boye sankon angon.

Daga bisani kuma duk sun janyo korafinsu inda su ka sasanta junayensu kowa ya kama gabansa.