Al’ƙawari ya cika – Ado Gwanja zai yi Wuff da Momee Gombe

Ga dukkan alamu, lokacin auren mawaki Ado Gwanja ya matso don da kan shi ya wallafa kyawawan hotunansa a Instagram da jaruma Momi Gombe inda ya rubuta “Time”, wato lokaci.

Ita ma jarumar ta wallafa hotunansu tare inda ta ce “Alhamdulillah”. Nan da ‘yan uwan aikinsa da mutane masu musu fatan alkhairi su ka bazama su na ta kora musu addu’o’i.

Sai dai babu wani bayani dangane da lokacin da za a yi auren, amma da alamu lokaci ya matso don jarumai ciki har da Ali Nuhu su na ta yi musu fatan alkhairi.

Jarumar Minal Ahmad wacce aka fi sani da Nana Izzar so tana ci gaba da shan caccakar akan zargin kashe auren Ado Gwanja da Maimunatu, Tashar Tsakar Gida ta ruwaito.

Wannan ya biyo bayan hawa sabuwar wakarsa da ta yi mai suna Warrrr a ranar Juma’a tana kwasar rawa, hakan ya tunzura mabiyanta su ka hau caccakarta.