Allahu Akbar Mutum miliyan hudu ne suka ziyarci kabarin Manzon Allah a cikin wata uku

Rahotanni sun bayyana akalla Mutum miliyan huɗu ne suka ziyarci Kabarin Manzon Allah SAW a Madina cikin wata ukun farko na shekarar Musulunci ta bana.

Daily Independent Hausa 24 ta rawaito cewa Shafin da ke kula da Masallatai Biyu Masu alfarma na Saudiyya na Makkah da Madina, Haramain Sharifain ne ya bayyana hakan a Facebook ranar Lahadi.

Kazalika shafin ya ce yawan wadanda suka ziyarci Raudah kuwa da ke cikin Masallacin Manzon Allah ya haura miliyan kamar yadda BBC ta wallafa.