Allahu Akbar Rayuwa babu Tabbas, Kimanin Mutane 6 ne Suka rasa Rayukansu a wajen daukar wata Amarya daga garin Hadeja zuwa Yalleman.

Gidan jaridar BBC hausa ta ruwaito Yadda wani Mummunan hadarin mota yayi Sanadiyyar Mutuwar kimanin mutum shida 6 a wajen daukar wata amarya daga garin hadeja zuwa yalleman.

BBC ta bayyana cewa wannan hadari ya faru ne a ranar lahadin data gabata a cewar Hukumar Yan sandan Nigeria reshen jahar jigawa.

Irin wadannan hadarurruka ba sabon abune kasancewar a kullum ana samun irin haka tana faruwa, sai dai mutum a kullum yakasance me neman tsari daga irin hakan, a karshe muna masu Addu’a Allah ya gafarta masu dama Muslimi baki daya.