An kai amarya gidan yari bisa dukan uwar-gida kan ribibin shiga gidan gaba a motar maigida

Wata amarya ta tsinci kanta a gidan yari bayan da ta sumar da kishiyarta sakamakon ribibin shiga gidan gaba a motar mijinsu.

Lamarin ya faru ne a Jihar Kano a makon da ya gabata, bayan da uwargidan ta shaida wa Babbar Kotun Shari’ar Muslunci da ke Kofar Kudun gidan sarki, ƙarƙashin Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola, inda tai ƙorafin cewa kishiyarta ta mata duka.

A cewar mai ƙarar, ba ta da lafiya, sai mijin nasu ya aiko da mota a kai ta asibiti, sakamakon ita ba za ta iya tuƙa tata motar ba.

Ta ƙara da cewa shigar ta motar ke da wuya, kwatsam sai ta ha kishiyar ta riƙe kofar motar ta na ce mata ta fito, sai ita kuma uwargidan tace mata ba za ta fito ba saboda asibiti za a kai ta.

“Kafin ka ce kwabo, sai na ji ta doke ni a goshi na, nan na faɗi a sume, shine a ka garzaya da ni asibiti,”

Sai dai kuma amaryar ta musanta laifin na ta.

Daga nan ne sai Sarki Yola ya sa a ka aike da ita zuwa gidan yari zuwa mako mai zuwa domin ci gaba da shari’ar.

News All.