An kama matar da take shiga cikin daji da ‘yam mata tana kaiwa ‘yan bindiga suna lalata da su

Wata Mata ta bayyana yadda take kai wa ’yan bindiga ’yayan ta da ’yayan ’yan uwanta bayan da rundunar ’yan sanda ta musamman dakw yaki da ’yan fashin daji da ’yan ta’adda sun samu nasarar cafke ta tana tsaka da wannan aika-aika.

Kamar yadda Aminiya ta ruwaito cewa, Matar tana yiwa ’yan bindigar safarar ’yan mata zuwa Dajin Galadimawa ana aikata alfasha da su.

Rundunar ’yan sandan ta IRT wadda Babban Sufeton ’yan Sandan Najeriya ya kafa, ta titsiye matar inda ta bayyana yadda son zuciya ya rufe mata idanu ta shiga wannan harka.