An kama ‘Pastor’ da ya yi wa ‘yan gida daya su uku fyade

Wata kotun Majistare da ke zamanta a birnini Ilorin na jihar Kwara ta umurci da a tsare Pastor Makanjuola Olabisi bisa zargin ya yi wa wasu ‘yan mata su uku ‘yan gida daya fyade a Ilorin.

Punch ta ba da labarin cewa an tsare likamin cocin ne bayan da aka zarge shi da lalata da yaran ne, laifin da ya ci karo da dokar Penal Codd ta jihar Kwara.

Rahoton ‘yan sanda ya nuna cewa Paston na yi wa yaran wa’azi ne a duk lokacin da suka ziyarci cocinsa da ke Agba Dam, cikin Ilorin.

News All ta samu labarin cewa likamin cocin ya gayyaci babbar yayar ‘yan matan domin ta je wata ibada ta musamman, amma ta kiya, sai daga bisani aka gano ashe dama ya neme ta da soyayya ta kiya, a hankali dai har ya samu nasararta da kannenta biyu.