An Karrama Dan Sandan Da Ya Ki Amsar Cin Hanci Naira Miliyan 130 A Kano

Sufeta-Janar na ‘yan sanda, Usman Alkali Baba, ya karrama DPO na ofishin ‘yan sanda da ke Nasarawa, Kano, SP Daniel Itse Amah da lambar yabo saboda kin amsar cin hanci Naira Miliyan 130 da aka ba shi don a hada baki a kashe wata magana.

Amah, wanda aka ba da rahoton an ba shi cin hanci Dala 200, daidai da Naira Miliyan 130 don ya kashe wata magana da ta kunshi fashi da makami da zamba cikin aminci da aka yi wa wasu ‘yan kasuwa har Naira miliyan 350, 500 a Kano, ya amshi lambar yabon ne a Abuja a karshen mako.

Jaridar The Nation ta ba da rahoton cewa, lamarin fashi da makamin ya hada da wasu ‘yan sanda da kuma wani Lauya da ake kira Ali Zaki, wanda yanzu suke tsare a Abuja.

A kwanakin baya jaridar Sahelian Times ta wallafa labarin yadda Ali Zaki da wani Manajan Banki suka hada kai da wasu bata-garin ‘yan sanda suka kwacewa wasu ‘yan kasuwa kudi har Naira miliyan 350. Daniel da maganar ke hannunsa ya ki amsar toshiyar baki a binne maganar.

A cikin wasikar yabon da IG Baba ya aika wa Amah, ya yaba masa da kwarewar aiki da jarumar da ya nuna wajen yi wa Barista Ali Zaki da kuma. wasu ‘yan sanda da suka hada baki za su kashe maganar kamun kazar Kuku

Binciken da wata rundunar da Daniel Amah ya jagoranta ce ta kai ga kama wadanda ake zargin, yayin da aka mai da maganar zuwa hedikwatar ‘yan sanda da ke Abuja daga Kano bisa umarnin IG Alkali Usman Baba.

Kakakin rundunar ‘yan sanda, CSP Olumuyiwa Adejobi, ya tabbatar wa majiyar tamu kama Lauyan da kuma’ ‘yan sandan.

Kafin a canza masa wajen aiki, Daniel Amah shi ne DPO na Bompai, daga bisani aka mai da shi Nasarawa, kafin nan jama’a suna yabonsa da gaskiya da rikon amana.

News All