An Nada shahararren dan bindiga Sarauta a Jahar Zamfara a matsayin sarkin Fulani

An yi ta murna a garin Tsafe yayin da Sarkin ’Yandoton Daji a Jihar Zamfara, Aliyu Marafa ya nada wani shugaban ‘yan fashi da makami mai suna Adamu Aliero-Yankuzo, wanda aka fi sani da Ado Alero, a matsayin Sarkin Fulanin masarautar.

Bikin dai ya zo ne bayan shekara biyu da ‘yan sanda suka bayyana cewa ana neman shugaban ‘yan ta’addan tare da sanya masa ladan Naira miliyan biyar.

Mista Alero shi ne shugaban daya daga cikin kungiyoyin marasa tausayi da ke da alhakin kashe-kashe da nakasa da kuma garkuwa da mutane a kananan hukumomin jihohin Zamfara da Katsina.
Wani dan jarida mai suna Abdul Balarabe ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar da ta gabata a daidai lokacin da ake shagulgulan bikin baje kolin babur.“Daga karshe, shahararren dan fashin nan mai suna Ado Aleru ya nada shi Sarkin Fulani (Sarkin Fulani) na masarautar Yandoton Daji a jihar Zamfara. Wanda ya faru da misalin karfe 3:30 na yammacin yau Asabar 16 ga Yuli, 2022.

“Ado Aleru shi ne shugaban ‘yan bindigar da ke addabar al’ummar Katsina da Zamfara.