An Samu Zaman Lafiya Da Ƙwanciyar Hankali A Jihar Katsina, Cewar Alhaji Ibrahim Katsina

An Samu Zaman Lafiya Da Ƙwanciyar Hankali A Jihar Katsina, Cewar Alhaji Ibrahim Katsina Daga Comr Nura Siniya Mai baiwa Gwamnan jihar Katsina shawara kan harkokin tsaro, Alhaji Ibrahim Katsina, ya ce a cikin ƴan ƙwanakin nan jihar Katsina ta samu kwanciyar hankali, duk da hare-haren da ‘yan bindiga suke kaiwa a wasu yankunan jihar. Alhaji Ibrahim, ya bayyana cewa ayyukan ƴan bindigar ya ragu matuƙa inda ya alaƙanta wannan nasarar akan ƙoƙarin gwamnatin jihar da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki da sauran al’umma suke yi a koda yaushe kamar yadda Kamfanin dillancin labarai NAN suka ruwaito. Haka zalika Alhaji Ibrahim, ya ƙara da cewa daga ƙididdigar da suke da ita da kuma jawabai da suke samu a kullum, ya nuna cewa yawan laifuka a jihar gaba daya, ya ragu da sama da kashi 60 cikin ɗari”.Ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta sanya mata da yawa a harkar tsaro kuma ta fahimci cewa masu aikata laifuka sun fi sauraron mata idan aka lallashe su akan su guji aikata miyagun laifuka.A ƙarshe mai baiwa Gwamnan shawara, ya ce biyo bayan nasarorin da aka samu a harkar tsaro a jihar, a kwanakin baya gwamnatin jihar katsin ta mayar da ‘yan gudun hijira sama da 12,000 gidajensu a kauyen Shimfida na karamar hukumar Jibia.