An yanke wa su Mubarak Uniquepikin hukuncin sharar Kotu na tsawon wata guda

Kotun majistiri mai lamba 58 da ke No man’s-land a Kano ta yanke hukuncin share kotun na tsawon wata guda.

Da kuma biyan tarar dubu goma-goma ga tuhume-tuhume biyu da aka yi musu, sannan da bulala ashirin.

Sannan su wallafa sabon bidiyo su nemi afuwar Gwamnan.

Matasan biyu dai an zarge su ne da bata sunan Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje a wani faifan bidiyo da suka fitar