Ana Rade radin cewa Soyayya ta barke a Tsakanin Mawaki Rarara da Yar gidan Marigayi Rabilu Musa ibro Ummi

Wasu hotunan Dauda kahuta Rarara kenan tareda da daya daga cikin jaruman masana’antar shirya fina finan hausa ta Kannywood Ummi ibro kuma yace ga marigayi Rabilu Musa ibro.

Jarumar itace ta wallafa wannan hotuna a shafinta na Instagram inda bata bayyana komai akan hotunan illa kawai ta sanya alamar zuciya a kasan hoton.

Hakan yasa jama’a suka ringa yawo da Hotunan inda wasu ke masu fatan Alkhairi wasu kuma na tamabayar shin gaske don kuwa kun dace.