Ana zargin wata jaruma a masana’antar Kannywood da gartsawa wani yaro mai suna Aliyu, mai shekaru 11 cizo bayyan ta lallasa shi.
Kamar yadda bayanai daga bakin yaron da mahaifiyarsa su ka nuna, lamarin ya faru ne a anguwar Badawa da ke cikin Jihar Kano.
Yaron ya shaida wa Dala FM cewa tsegumi aka kai wa jarumar cewa ya kira ta da karuwa, wanda hakan ya hassala ta ta bukaci ya zo shi kuma yaki zuwa.
Da alamu hakan ya yi matukar bata mata rai daga nan ta kamo hanya ta nufi har inda yake ta dinga gaura masa mari har sau bakwai.
Bayan an yi yunkurin raba su ta fusata ta samu gadon bayansa ta gannara masa cizo.
Mahaifiyar yaron ta bayyana cewa jarumar ta fito a matsayin ‘yar sanda a fim din Sirrin Boye.
Sannan ta bukaci a bi musu hakkinsu. Da alamu marin ya yi matukar ratsa yaron don wanda ya tattauna da shi ya duba yadda idon yaron ya sauya kala tare da ganin yadda cizon ya ratsa bayan yaron.

Leave a Reply