Ango ya fice daga gurin ɗaurin aure bayan gano Amaryar nada yara 4

An baiwa ango haƙuri

A wani ɗan gajeren bidiyo, anga yadda wani ango ya fice daga gurin ɗaurin aure, a yayin da jama’a da dama suka biyo shi suna ta ƙoƙarin bashi haƙuri. Haka nan, an hangi amaryar tana ta sharɓar kuka a yayinda wasu gungun mata ke ƙoƙarin rirriƙeta.

A wani ɗan guntun bidiyo da aka ɗora a Instagram wanda kuma ya karaɗe kafafen sadarwa na zamani, anga angon ya fito a fusace yana ta kumfar baki, a lokacin da wasu gungun mutane keta ƙoƙarin bashi haƙuri.

Amarya bata faɗa mishi gaskiya ba kafin ɗaurin auren

Ango ya bayyana cewa amaryar bata taɓa faɗa mishi cewa tana da ‘ya ‘ya ba sai a yanzu da aka zo wajen ɗaurin auren nasu.

“A duk tsawon shekarun da muka ɗauka tare bata taɓa faɗa mun cewa tana da yara ba sai yanzu. Sai yanzu take faɗa mun wai cewa tana da ‘ya ‘ya huɗu.” inji angon.

Amarya nata sharɓar kuka

Amaryar dai babu abinda take yi face sharɓar kuka tana faɗin cewa ta shiga uku, bata san yaya zata yi ba, a yayin da suka kuma wasu mata keta ƙoƙarin lallashinta.

Mutane da dama dake gurin sunyi iya bakin ƙoƙarin su wajen ganin sun daidaita lamarin, amma dai da alama ango yana cikin matuƙar ɓacin rai.

Wannan dai ba shi bane karo na farko da ake samu irin wannan. A lokuta da dama wasu matan kan ɓoye wa mazajen da zasu aura wata rayuwar tasu ta can baya da suka gudanar. Wasu mazajen kan gano amma sai su haƙora, wasu kuma su ɗauki mataki.

Wasu matan kuma ma sukan haɗa wata ɓoyayyar rayuwar ta daban da kuma soyayyar mazajen da zasu aura na haƙiƙa. Hakan ma na daga cikin abubuwan da sukan kawo matsala a duk lokacin da mazajen suka gano.