Auran kanwata da mijina yayi ya kara mana kaunar juna da dankon zumimci, cewar wata uwargida wacce mijinta ya auri kanwar ta News All…

Desire Cipimo, wani matashi ne da ya auri mata 2 wadanda uwarsu daya uba daya kuma ba tagwaye bane, kamar tadda “Labarun Hausa” suka ruwaito taruwaito.

Mutumin ya fada tarkon soyayyar ‘yan uwan junan wanda shi din shugaban kauye ne, kuma har sun haifi yara 10.

Yayin tattaunawa da Afrimax English, Desire ya bayyana yadda ya auri matarsa ta farko mai suna “Goreth” inda suka haifi yara biyu amma daya ya kwanta dama a ranar zagayowar haihuwar sa.

Bayan shekaru 12 ba tare da ta kara haihuwa ba, mutimin ya auri matarsa ta biyu wacce kanwa ce ga matarsa ta farko “Mawazo” wacce yanzu haka yaransu 9 da ita.

Shekarun dan Desire na farko 32 yayin da autan sa ke da shekaru 2 a duniya.

Mutumin ya bayyana cewa: Muna ta kokarin haihuwar wasu yaran amma abin yaci tura duk da yadda muka dinga neman magunguna iri-iri, hakan yasa na auri kanwarta, a cewar Desire.

Goreth tace: bata daukar kishiyarta a matsayin kishiya face kanwa, Kuma auren su da mijin yayi ya kara musu karfin zumunci.

Yanzu haka suna ayyukan gida tare da kuma tallafa wa mijinsu don taso da yaransu, hakan yasa Goreth ta shawarci mata da su dena nuna wa kishiyoyinsu kishi sai soyayya.

Don miji yana son ki ko da ya auri wata zai cigaba da nuna miki kula wa da soyayya ako da yaushe, don haka ku
dinga baiwa maza damar su, a cewarta.

Rahoto daga👉 Labarun Hausa