Ba Don Ƙoƙarin Shugaba Buhari, Da Ƙasar Laberiya Bata Zauna Cikin Kwanciyar Hankali Ba – George weah

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na tabbatar da dimokuradiyya a fadin kasa nan, yana mai cewa Najeriya na kokarin ganin an gudanar da sahihin zabe a babban zaben shekarar 2023.mai zuwa.

Buhari ya bayyana hakan ne a ranar Talata a kasar Laberiya yayin da yake ganawa da sauran shugabannin kasashen duniya domin halartar bikin cika shekaru 175 da samun ‘yancin kan kasar dake yammacin nahiyar Afirka.

Shugaba Buhari ya yi kira ga takwarorinsa na Afirka ta Yamma da su yi duk mai yiwuwa wajen ganin an gudanar da zabe a kasashensu cikin aminci da walwala da gaskiya domin ta haka ne kadai za a iya kare yankin daga bala’in da ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar. Da kuma hare-haren da yayi kamari a kasashe uku kwanan nan.

A cewar shugaban, dole ne dimokuradiyya da shugabanci na gari su sami wanzuwa a nahiyar Afirka don dorewar zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaba, yayin da shugabanni su kara zage damtse wajen tabbatar da dorewar dimokradiyyar a nahiyar Baki daya.

Buhari ya kuma yabawa takwaransa na kasar Laberiya, Dokta George Manneh Weah, bisa nuna kaunar kasarsa da tabbatar da zaman lafiya da hadin kai da ci gaba, kamar yadda ayyukan da suka shafi al’umma da aka aiwatar da manufar kai kasar zuwa ga kololuwa. a cikin karancin albarkatun da take da su, yayin da ya bukaci shugaban na Laberiya da ya kara himma, tare da ba shi tabbacin ci gaba da goyon bayan Najeriya.

Anashi bangaren shugaban kasar Laberiya, Dr. George Weah, ya godewa shugaba Buhari da sauran shugabannin kasashen yammacin Afirka bisa halartar taron da suka yi, inda ya ce idan ba don Najeriya ba, ba za a samu zaman lafiya a Laberiya ba