Babu wata soyayya tsakanina da Hamisu Breaker inji Fatima Ali Nuhu
Lallai baya ta haihu inji hausawa yanzu duk yadda ake ta yada labarin cewa fitaccen mawaki Hamisu Breaker zai amgon ce tare da babbar yar sarki Ali Nuhu Yanzu abin ya zama labarin kanzan kurege tunda gashi magana ta fito daga bakin masu abin wato Fatima Ali Nuhu.
Ta bayyanawa Duniya cewa wannan labarin da yake ta yawo a shafukan saba zumunta na zata angonce da mawaki hamisu breaker ashe dai labarin babu shi kawai kagashe akayi domin hakan ba sabon abu bane an saba.
Matashiyar budurwar ta ƙaryata hakan kuma tayi kira ga mutane dasuyi watsi da wannan labarin wanda bashi da makama balle tushe tace bata da wata babbar alaka wacce har takai ga maganar soyayya.
Lallai wannan abu da ban mamaki yake yanzu ace yadda wannan labarin ya karade ko ina ashe daman karya ne yanzu dai zamuga yadda mutane zasu gamsu da wannan sabon labarin da yake fitowa da dimi diminsa
Daman kuma tunda aka fara wannan danbarwa babu wanda yayi magana Acikin su sai yanzu da ita ta fito da kore wannan labarin daga kanata yanadai dakyau jama’a su dinga lura wajen tantance labari kafin su yarda

Leave a Reply