Ban da burin da ya wuce kowa a duniya ya san ni, Sadiq Saleh, Mawaƙin ‘Abin ya motsa’

Sadiq Saleh, sabon mawaki wanda ya samu shahara bayan sakin wakarsa mai taken ‘Abin ya motsa’ ya bayyana burinsa a rayuwa inda yace yana son ko ina a duniya a san shi, kuma yanzu haka ya fara taka matakin.

A tattaunar da BBC Hausa tayi da matashin mai karancin shekaru, ya bayyana tarihinsa inda yace an haife shi a Maiduguri kuma ya taso sannan ya yi karatunsa a can.

Ya ce ya kwashe shekaru yana yin waka kasancewar tun yana karami yake da burin zama mawaki, daga nan kuma ya hadu da abokai masu irin ra’ayinsa.

A cewarsa, ya yi wakoki na siyasa da na aure daban-daban kuma bai samu shahara bane sai a wannan sabuwar wakar da yayi ta Abin ya motsa, wacce kowa ya san shi da ita.

Yayin da aka tambayeshi wakar da yafi so a duk wakokinsa, ya ce yafi son wakar Abin ya motsa, sai dai ba ita bace wakar da yafi shan wahala yayin rerata.

Ya ce wakar aure ta farko da yayi ne yafi wahala yayin yin ta. Ya shaida cewa ba ya da wani buri da ya zarce kowa na duniya ya san shi, kuma yanzu haka da alamu ya fara taka wannan mataki.