Bashin Da A Ke Bin Najeriya Ya Kai Naira Tiriliyan Hamshin

Bashin Da A Ke Bin Najeriya Ya Kai Naira Tiriliyan Hamshin Daga Yunusa Abdullahi Yayin Da Gwamnatin Tarayya Za Ta Gabatar Da Kasafin Naira Tiriliyan 11.3 a 2023.A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne gwamnatin tarayya ta ce Najeriya za ta sake ciyo rancen wani giɓin kasafin kuɗi na Naira tiriliyan 11.3 a shekarar 2023, wanda hakan zai sa basussukan da a ke bin ƙasar su kai Naira tiriliyan 50.Ministar kuɗi da tsare-tsare ta ƙasa, Zainab Ahmed, ta ce gwamnatin ƙasar na shirin kashe Naira tiriliyan 19.76 a shekara mai zuwa, wanda daga ciki gwamnati za ta iya tara Naira 8.46 ne kawai ta hanyar sayar da man fetur da sauran kuɗaɗen shiga.Ta bayyana hakan ne a yayin da take jawabi a zaman kwamitin majalisar wakilai kan kasafin kuɗi na shekarar 2023-2025 a Abuja da yammacin ranar Litinin.Ministar ta ce Naira tiriliyan 1.9 za ta fito ne daga hanyoyin da ke da alaƙa da mai yayin da ma’auni zai fito daga wuraren da ba na mai ba ne.Ta ce za a tsara kasafin ne kan dala 70 a kan kowacce ganga ta ɗan yen mai da kuma canjin N435.57 zuwa dala.Ministar ta ce ana samar da man fetur a shekarar 2023 akan ganga miliyan 1.69 a kowace rana; Haƙiƙanin haɓakar GDP na kashi 3.7 cikin ɗari da hauhawar farashin kayayyaki na 17.16 bisa ɗari na shekara.Ta yi nuni da cewa tallafin man fetur zai ci gaba da kasancewa har zuwa tsakiyar shekarar 2023 zuwa ga ƙarin watanni 18 da aka sanar a farkon shekarar 2021.Ministar ta ƙara da cewa za a bayar da Naira tiriliyan 3.36 domin biyan tallafi a shekarar 2023.Ministar ta kuma shaida wa taron cewa za a tsaurara matakan aiwatar da tsarin gudanar da ayyuka na Kamfanoni Mallakar Gwamnati wanda zai ƙara haɓaka rarar kuɗaɗen da ake fitarwa a shekarar 2023.Ministar ta ba da tabbacin cewa babu wani hasashen cewa Najeriya za ta gaza wajen biyan basussukan da take yi nan gaba kaɗan.Ta kuma ba da tabbacin cewa, yayin da adadin kuɗaɗen da ake amfani da su a halin yanzu wajen biyan basussuka ya yi sama da faɗi a kasafin kuɗin 2022, an samar da tsare-tsare don tafiyar da lamarin.Mun shirya cewa kashi 60 na kuɗaɗen shiga za a kashe ne wajen biyan basussuka, amma a wasu watanni, rabon ya haura zuwa kaso 90 cikin 100.A gaskiya muna bin dabarun kula da bashi na matsakai ta, ba a karɓar basussukan da gangan saidai domin yiwa ƙasa hidima. Ministar ta amince, duk da haka, gwamnati na fuskantar matsin lamba don tafiyar da ayyukan basussuka sakamakon raguwar samar da kuɗaɗen shiga. Ministar ta yi kira ga Majalisar Dokoki ta ƙasa da sauran masu ruwa da tsaki da su shigo cikin gwamnati domin ƙara samun kuɗaɗen shiga.Muna da matsin lamba dangane da rabon saboda lokacin da kuɗaɗen shiga ba su yi aiki ba, yana nufin muna da matsalolin samun damar yin hidima ga dukkan ayyuka na gwamnati, halin rashin ruwa yana da ƙalubale sosai. Don haka abin da ya kamata mu yi, ciki har da majalisa, shi ne yin aiki don ƙara yawan kuɗaɗen shiga.Ta ƙara da cewa muna yin hakan kuma mun fara ganin ci gaba, amma muna buƙatar ci gaba da tura sandar,” in ji ta.Shugaban kwamitin kuɗi na majalisar James Faleke (APC-Lagos) ya ce kowa ya san halin da Najeriya ke ciki ta fuskar samar da kuɗaɗen shiga.Mista Faleke ya bayyana cewa Najeriya na fama da ƙarancin kuɗaɗen shiga, kuma abubuwa da dama suna shan wahala idan kuɗaɗen shiga ya yi ƙaranci. Ofishin kula da basussuka ya bayyana a baya cewa bashin Najeriya a watan Disamba na 2021 ya kai Naira tiriliyan 39.55.