Bayan kashe ummita shugaban yan China na Nigeria yaje fadar Sarkin Kano domin yi masa ta’azzziya
Lallai wa’yannan mutane dason zaman lafiya suke ana ganin sunyi hakane domin tsadar da rayukan rahowar yan uwansu dake Kano don gujewa fushin mutane wajen daukar fansa akan wannan matashitar budurwa wacce wannan san Chinan yayi sanadiyar barinta duniya ta hanyar chaka mata wuka
Sunyo tattaki daga jihar Abuja domin bawa Sarki hakuri akan wannan al’amari daya faru na kashe wannan baiwar Allah wanda sunsan mutane ransu ya ɓaci kwarai da gaske
Shugaban na yan China ya fara da bawa mutane Kano gaba daya hakuri da neman tafiyarsu akan wannan abu sannan ya tabbatar musu dacewa baza susu hannu ba zasubar hukumar Shari’a ta aiwatar da aikin ta batare da yi musu katsalandan ba
Shima anasa bangaren sarki ya jajanta faruwar wannan abu kuma yace zasu zuba ido domin ganin an hukunta wannan mutumin saboda Wannan abinda ya aikata mai munin gaske wanda duka mutane suke Allah wadai
Hakika hankalin iyayen wannan yarinyar ta kwanta tunda sukaji kowa na cewa za’a hukunta wannan mutumin saboda a kullum fatansu shine ayi musu adalci kuma sunga Akwai alamun nasara acikin Shari’ar

Leave a Reply