Bayan shafe shekaru 67 a gidan yari an sallami wani tsoho da aka tsare tun yana dan shekara 15 amma yace ba inda zashi

Wani tsoho da ya shafe shekara 67 a gidan yarin  Philadelphia, bayan an yanke masa hukuncin daurin rai da rai, ya nuna turjiya ta kin fita daga gidan yarin, bayan an sallame shi an yi masa afuwa. 

Dalilin zuwan tsohon gidan yari

Tsohon mai suna Joseph Ligon, an daure shi ne tun yana ɗan shekara goma sha biyar, a sakamakon zargin kisan wadansu  mutane biyu. Tun daga wancan lokaci Ligon ya rasa yancin sa na walwala. 

A ranar  20 ga Fabarairun shekara ta 1953,  a  wajen wata liyafa, Ligon din da abokansa hudu suka  yi wa mutane takwas fashi, inda suka kashe  biyu daga cikin su  har lahira.

Duk tsawon wannan lokaci , Ligon bai tura takaddar neman  afuwa ba, wacce ita  zata sa a sake shi daga gidan yarin, tare da sanya ido akan sa domin tabbatarda  ganin bai sake shiga cikin wata matsala ba.

Baiyi tsammanin za’a iya yi masa afuwa ba

 A cewar lauyansa, bai mika takardar neman afuwan  ba ne saboda bai yi tunanin ya cancanci a sake shi ba, inda  ya shafe shekaru 67 a gidan yari.

Har’ila yau, ya sake samun wata dama a shekarar 2016, amma sai ya gaza yin amfani da ita, saboda tunanin da yake dashi a baya na cewa bazai iya samun sassauci ba. 

Idan aka sallami Joseph Ligon, zai tafi ya gudanar da rayuwar sa ba tare da sanya idon hukuma akan sa ba. Amma ya ki karbar afuwar da aka yi masa, bayan abokan zaman sa fursunoni sun amshi tasu afuwar da hannu biyu. 

yana jin kurkuku tamkar gida a gareshi

Kasantuwar ya dade a gidan yarin, wadansu ma na ganin cewa bazai iya rayuwa a wani wuri ba kurkuku ba.