Bayan shekaru 15 yana biyan kudin haya, miji ya fadi warwas bayan gano matarsa ce mai gidan

Wani mutum dan kasar Zambia mai suna Martin Stampa ya fadi kasa warwas inda ya sume bayan gane cewa ashe matarsa ce mai gidan hayar da su ke ciki, LIB ta ruwaito.

Manema labarai sun gano cewa ya kwashe shekaru 15 yana biyan kudin hayar kwacha 3500 duk wata. Sannan an gano cewa matar ce ke amsar kudin da sunan za ta kai wa min gidan.

Sai dai an gano cewa matar mai suna Lushomo ta yi hakan ne don ta hukunta mijin wanda ta fahimci cewa yana bin matan bariki.

An samu rahoto akan yadda Martin ya fada wa matarsa cewa ya samu wata budurwa a wajen aurensu kasancewar yana son mace mai tsananin kaifin kwakwalwa don su dinga tattaunawa da hira ta basira.

Wannan lamarin ya hassala Lushomo inda ta fallasa masa sirrin da ta dade tana boyewa. Ta sanar da shi cewa ba ya da kaifin kwakwalwa tunda ya kasa fahimtar cewa ita yake biya kudin haya duk wata don gidan da su ke ciki nata ne.

Bayan jin wannan ne Martins ya rikice ya fadi kasa warwas. Sai da mutane su ka samo ruwa su ka dinga watsa masa don ya falka