BIDIYO ZA’A DAURA AURE TSAKANIN IDRIS ME WUSHIRYA DA MURJA KUNYA -Lil Baba ya dauki Nauyi


Abin farin ciki ko kuma abin fada kuji yadda wannan mawakin yayiwa wa’yannan yan tiktok din wani alkawari abin birgeba yanzu zamuga matukar da gaske suke dole zasuyi idan kuma shashanci ne ya hadasu zasu cigaba da abinda da sukeyi da aure dai abin sone babu gaba dashi a duk wata mu’amala ta yau da gobe aure gaba yake da komai.

Tun bayanda aka kaiwa murja barazana wacce akace yan hisba suna neman ta bata da wani aboki wanda ya wuce Idris me wushirya akoda yaushe tare ake ganinsu har gida Yake Binta su fito su tafi sabgogin su kai kace abokintane tun na yarinya bayan kuma yaɗuwar kwanan nan ce

Anyi tunanin wannan abubuwan da suke yi soyayya ce bayan kuma ba soyayya bace kawai aminantakace tasa suka zama hanta da jini ma’ana koda yaushe suna tare kamar masoyan juna.

Ganin haka yasa Lilin Baba yace zaiyi musu aure ma’ana zai dauki duk wata dawainiya ta aure matukar wa’yannan Mutanen zasu yadda su auri junansu kuma har yanzu ba’aji sunce komai na yanzu haka su amince yanzu haka kuma suyi watsi da

wannan tayin mai albarka mutanen gari kowa yana magana yana cewa lallai ta wannan hadi yayi kawai su yadda su auri juna abin zaiyi kyau sosai

Mudai muna gefe kawai fatan mu shine Allah ya tabbatar da alkhairi yasa albarka aciki idan abin ya kasance