Bidiyon Rahama Sadau A Wajen Mosta Jiki Sanye da Damammen Wando Ya Jawo Cece-kuce

Labaran Kannywood

Bayyanar bidiyon fitacciyar jaruma Rahama Sadau lokacin da take wajen mosta jiki ya jawo cece-kuce a shafukan sada zumunta.

Mutane suna ta tofa albarkacin bakinsu bayan da sukaga an wallafa bidiyon jaruma Rahama Sadau tana motsa jiki sanye da kayan atisaye.

Wasu mutane suna nuna rashin jin dadinsu ganin kalar kayan da ta sanya lokacin da take mosta jiki inda suke alaqanta hakan da bai dace ga mace musulma ba ta shiga cikin maza sanye da wadannan kaya domin motsa miji tare.

Da yawa sun alaqanta hakan da sam sam bai dace ba, inda daga wani bangaren kuma wasu mutane suna cewa basu ga wani abun aibu ba na wannan abu da tayi kawai hali ne na mutanen mu komai suka gani bazasuyi shiru ba sai sunce wani abu.

Bugu da kari, cikin wannan bidiyo babu wata shiga ta rashin da’a da tayi na kayan da ta sanya domin kuwa har hula ta sanya da kuma dogon wando.

Amma dai duk da hakan baisa ta tsira daga martanin mutane ba saboda basu saba ganin irin wannan ba.

Ga bidiyon nan ku kalla mun kawo muku shi a kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *