Daga Salisu Magaji Fandalla’fih
Rahoton da muke samu ya tabbatar mana da cewa jami’an tsaro sun Kama fitaccen marubucin nan na Arewacin Najeriya mai suna Indabawa Aliyu Imam, Bisa Zargin ɓatawa Jarumin shirin kwana casain Sahir Abdul wanda aka fi sani da malam Ali suna.
Tunda fari Malam Ali ya shigar da matashin marubucin kara zuwa kotu ne bisa zargin bata masa suna tare da Jaridar Dailly Hausa.
A cewar malam Ali, Indabawa hadi da wasu kafafen yada labarai, sun bata masa suna a kafafen sada zumunta da sunan yana neman lalata da wata yarinya a kafar sadarwa ta Whatsapp, da zina dukda yarinyar an kusa Auren ta.
A cikin labaran da aka yaɗa an bayyana ayi hankali da Malam Ali domin mazina ci ne, tare da gargadin idan malam alin bai yarda ba yaje kotu, lamarin da ya kira da bata suna da kuma cin zarafi da ƙage.
A zantawar Lauyan Malam Ali da tashar tsakar gida ya bayyana cewa, Shi Indabawa ne da kansa ya nemi Malam Ali daya basu wani kuɗi, ko ya ɓata masa suna a kafafen Sada Zumunta, lamarin da Malam Alin yaki, inda shi kuma yai anfani da haka wajan yaɗawa cewa Malam Ali Mazinaci ne.
A cewar Lauyan bayan da malam Ali ya shigar da kara, Indabawa ya kirashi yace shifa maganar kudin da wasa yake, a cewar Lauyan muna da Muryar sa da dukkanin bayanan barazanar.
A karshe Lauyan yace tuni yan sanda sun kama, marubucin Indabawa Aliyu Imam sannan zai fuskanci Shari’a, Lauyan ya kara da cewa, dukkanin jaridar da suka buga wannan labari suma za’ai bincike kansu dan Tabbatar da sunbi hakkin Malam Ali ta inda ya dace.
Leave a Reply