Wani matashi ya wallafa wani bidiyo akan yadda dan uwansa da su ke tagwaye ya kai masa ziyara a makarantar da yake aiki a matsayin malami, Legit.ng ta ruwaito.
Yayin da dan uwansan ya shiga aji, dalibai da dama sun yi mamaki inda su ka dinga kallonsu kasancewar kamar tasu har ta baci.
Yayin da wasu su ke ta wahala wurin bambanta su, nan da nan wasu daliban masu dabara su ka duba kafafunsu inda su ka gane malaminsu da takalminsa.
A wani bidiyo wanda shafin @twindiaries na TikTok su ka wallafa aka ga bidiyon wanda ya dauki hankalin mutane da dama.
Daliban sun yi matukar mamaki kasancewar ba su taba sanin cewa malaminsu tagwaye bane sai a ranar.
Duk da halittarsu iri guda, haka kuma tufafin da ke jikinsu, amma abin ban mamakin shi ne takalminsu ya bambanta wanda hakan yasa su ka yi saurin gane malaminsu.
Leave a Reply