Da Wuya Kaga Dan Fim a Wurin Musabaqar Al’kura’ani Ko Saukar Al’kura’ani sai dai Wurin Taron bukukuwa – Adam zango.

Da Wuya Kaga Dan Fim a Wurin Musabaqar Al’kura’ani Ko Saukar Al’kura’ani sai dai Wurin Taron bukukuwa – Adam zango.

A kwanakin baya Dr. Idris Abdulaziz Bauchi, yayi Maganganu akan Yan fina-finan Hausa, inda Malam yace duka Yan film Babu Mai addin, Wanda jarumai da Dama suka fito suna ta mayar da martani ga malamin, abin dubawa anan shine dukkkanin masu mayar da martani ga malamin sunki gasgata abinda malamin ya fada

Sai da dazu da rana jarumi Adam A Zango ya fito ya gasgata wadancan kalaman dashi Dr. Idris ya fada.

Har najiyo Yana fadin da Dama mata jarumai dake masanatar su suke jawowa masana’antar irin Wannan Maganganun, saboda da yawa daga cikinsu Da rashin tarbiyyarsu suke fitowa daga gidajen iyayensu, su shigo masanatar..

Dama Abdurrazaq sultan, ya fada acikin wata tattaunawa da yayi da gidan Rediyon nasara cewa, “masana’antar Babu tarbiyya Sam acikinta, Kuma fina-finan Hausa suke Bata tarbiyya Yara…

Sultan ya Kara da cewa, “yanzu ba wasan Hausa Ake ba, wasa da Hausa Ake”

Ala hayya halin, naji dadi matuka gaya Dana ga wasu jaruman sun fara Gane gaskiya, Kuma Allah ya cigaba da ganar dasu

Zango dai yace bazaka taba Ganin Dan film agun musabaqar Alqura’ani, ko Saukar Alqura’ani ba, sai dai gun biki ko rasuwar waninsu, Shima sai dai ya kasance babban jarumi