Dalilin da yasa na janyo matata harkar fina-finan Hausa inji Haruna Talle mai fata

Dalilin da yasa na janyo matata harkar fina-finan Hausa inji Haruna Talle mai fata

Wasu mayiwa wannan al’amari na wannan jarumin kamar cin fuska da kuma bata al’ada da addini domin wannan abun da yayi adai Nigeria babu wata kabila da zatayi irin wannan abun domin yanzu yadda duniya ta lalace kowa yana kishin iyalansa

Jarimin dai ya shigo da matarsa cikin sana’ar film wanda abin sai ya zama wani banbakwai dan ba’a taba gani ba a kasar Hausa mutum da matarsa dukansu suna sana’ar film al halin kuma da akwai aure a tsakaninsu

Acikin wannan bidiyon a zantawar da akayi dashi yace shifa atunaninsa wannan kamar cigabane ya kawo duk wani dan filma matarsa tanada matukar kishi akansa saboda yadda take ganin mu amalarsa da sauran mata yan kannywood

Kuma matan jatuman kannywood suna da yawan zargi akan mazajen nasu amma anasa tunanin hakan da yayi zaisa wa’yannan abubuwan su ragu suma takan su fahimci a haka sana’ar take

Inda yace yanzu kamar kasar India a mace tana da aure ma tana yin film koda kuwa mijinta ba dan film amma mu hakan kamar kauyancine sai dai ya manta da al’adar kasar India da kuma ta kasar Hausa akwai banbanci ba kadanba