Dalilin Dayasa Adam A Zango Yafi Kowane Jarumi Masoya A Kannywood

A labarin da muke tattarowa ya nuna mana cewa Adam zango shine jarimin da yafi kowanne jarumi yawan masoya a kannywood.

Kalli jama’ar da Adam zango ya tara shine jarimin da yafi kowanne jarumi yawan masoya a kannywood.

Jaruman daman yayi sanarwar cewa zaiyi wasannin acikin wannan watan na ogoster wanda tun daya ga wata aka fara gabatar da wannan wasanni kuma suna kayatar da masoya da masu kallo inda dubban mutane ke zuwa kallo.

Wasan da ya gabatar jiya da yamma shine wanda yafi tara mutane fiye dana ragowar ranakun wanda mutane tsabar yawa harda rasa wajen zama yayinda suka dinga tsayawa a tsaye duk dan su kalli jarumin me farin jini.

Anyi kididdiga cewa jarumi Adam Zango shine jarimin da yafi kowanne farin jini domin indai ba shiba babu wani jarumi daya isa ya tara wannan al’ummar masu dinbin yawa.

Hakan wasu naganin ai maimakon masoyan sa su ragu kullum kara karuwa suke sai kara cinye masoya yake a duk kannywood shine bahaushen da akace yafi kowa suna a fadin Nigeria.

Jarumin yace a kullum yana alfahari da masoyansa sune gatansa dasu yake tutiya a koda yaushe bashi wani gata sai masoyansa.