Dama na Auri junaidiyya a rayuwar gaske cewar Alhaji Badamasi
Babban Alhaji na cikin shiri mai nisan zango wanda arewa24 suke haskawa mai suna gidan badamasi ya fadi magana wacce ta bawa mutane mamaki da kuma daukar hankalin su wacce harma ake ta yi masa fatan Allah ya tabbatar.
Alhaji Badamasi yace yana fatan dama ya auri junaidiyya a gaske ba a cikin dirama a kwanaki dai anyi rade raden cewa an daura aure tsakanin Alhaji badamasi da kuma junaifiyya gidan badamasi sai dai kash ashe duk karya ce ta mutane
Anya hakane yayin daukar shirin film din gidan badamasi wanda ta fito a matarsa shine hakan ya dauki hankalin mutane suka dinga ganin hakan kamar a gaske.
Sai Alhaji badamasin awata Shira da akayi dashi yayi fatan daman hakan ya kasance dashi a gaske ya auri yarinyar domin yace ai kyakkyawa ce kuma tana da hankali daadabi da biyayya ya memi mutane dasu taya shi da addu’a domin ganin ya sameta a gaske
Sai dai wasu na Allah wadai da wannan kalaman nashi inda suke cewa me zatayi dashi ai yayi mata tsufa ganin cewa ita yarinya ce jagab shi kuma gashi tsoho kuma idan ma zata auri tsohi ai shi bashi da yawan kuɗaɗen da zata aure shi
Sai dai wasu na cewa Allah ya tabbatar da hadin nan a gaske muga yadda yan bakin ciki zasu mutu
Leave a Reply