Duniya Tazo Karshe: An Kama Wani Magidanci Yana Kwana Da ‘Yar Cikinsa Saboda Kyawunta

Wani magidanci dan shekaru 53 da haihuwa, mahaifin wata ‘yar shekaru 13 ya bayyana wata kotun majistiri da ke garin Ogba a jihar Legas yadda ya share shekara uku yana kwana da yarinyar ‘yar cikinsa.

Mahaifin mai suna Promise Eshiet ya bayyanawa kotu tsananin kyawun ‘yarinyar nasa ne ya rinjaye shi ga aikata abun kunyar inda ya kuma dogana laifin da sharrin shedan.

Eshiet ya shiga hannun ‘yan sanda ne bayan da ‘yar nasa ta kasa cigaba da jure cin zarafin da ya ke mata wanda ya fara a tun lokacin da ta ke shekara 10 a duniya.

Yarinyar ta bayyana cewa mahaifin nata ya keta mata haddi ne tun a lokacin da bata san me rayuwa ya ke ciki ba, kuma ya cigaba har na tsawon shekara uku.

Mai gabatar da karar Mr Christopher John, ya ce mumunan al’amarin da ya faru tsakanin Eshiet da ‘yarsa abun kunya ne da ya sabawa tsari na mutuntakr dan Adam ganin cewa shine asalin mahaifin yarinyar.

Majistirin bayan sauraran karar ya bada odan cigaba da tsare Eshiet tare da tura fayil dinsa zuwa DPP zuwa wani lokacin da DPP za ta shawarce su kan hukuncin da yakamata a yanke masa inda aka kuma tura yarinyar asibiti domin binciken lafiyarta da sanin irin ta’adin da uban ya mata.