Fasto ya mutu bayan ya sa an birne shi a kabari inda ya sha alwashin zai tashi irin yadda ‘Jesus’ yayi

  • Wani fasto a kasar Zambia ya rasa ransa bayan an birne shi a kabari na tsawon uku
  • James Sakara, ya dade yana bayyana cewa zai tashi bayan ya mutu irin na ‘Jesus’
  • Sai dai banyan an dawo an duba kabarin, an tarar da shi a mace kamar yadda majiyoyi su ka bayyana

Wani fasto a kasar Zambia ya mutu bayan ya yi yunkurin mutuwa kuma ya tashi kamar yadda Jesus yayi, Daily Mail ta ruwaito.

Hakan yasa yasa a daure hannayensa sannan aka birne shi a kabari na tsawon kwana uku.

An tsinci gawar James Sakara, mai shekaru 22, bayan komawa don a hako kabarin a garin Chadiza da ke Zambia, wani yanki na gabashin kasar.

Sakara, fasto ne na cocin Zion, kamar yadda rahotanni su ka bayyana, kuma kafin ya nemi a birne shi, sai da ya janyo aya daga cikin Bibul sannan ya nemi a rufe shi.

Mutane ukun da ya bukaci su daure masa hannayen, sun daure shi dakyau sannan su ka birne shi a kasa, inda ya kwashe kwana uku.

Bayan haka kabarin ne aka ga gawarsa don shirin dawowarsa da ransa bai tabbata ba.

A cikin mambobin cocin da su ka taimaka wurin rufe faston, daya ya mika kansa ga ‘yan sanda.

Har yanzu ana ci gaba da neman sauran wadanda ake zargin sun tsere.

Faston ya mutu ya bar matarsa da ciki kamar yadda rahotanni su ka nuna.