Gajiyar tafiya ce, Martanin Fati Bararoji akan hotonta wanda aka ganta a komade

A safiyar jiya ne aka dinga yada wasu hotunan tsohuwar jarumar Kannywood, Fati Bararoji wacce tayi tashe a kwanakin baya a soshiyal midiya inda aka ganta duk ta komade, Fim Magazine ta ruwaito.

A yadda aka santa da cikarta da surarta, a hotunan duk an ga yadda ta zaizaye ta tsiyaye sannan tsufa ya fara bayyana karara a fuskarta, inda wasu su ka dinga zargin ciwo ne ya tasa ta gaba.

Sai dai Mujallar Fim ta nemi sanin karin bayani har wurin ita jarumar, inda aka zargi ta yi ciwon, ashe ba haka abin yake ba. An gano cewa jarumar ta wallafa hoton ne a status din TikTok dinta, wanda tun daga nan mutane da dama su ka dinga yadawa har da masu mata fatan samun lafiya akan cutar da ke damunta.

Yayin da Mujallar fim ta kirata a waya, ta bayyana cewa:

Na yi mamakin yadda naji mutane na ta surutai kala-kala akan hotunana. Har da masu cewa ba ni da lafiya. To ni lafiya ta kalau kuma ban yi fama da wani ciwo ba.

Na dai san na yi tafiya zuwa Abuja, daga can na wuce Sokoto don halartar wani biki, daga nan na dawo Kano.

Yanayin tafiyar da kuma gajiya ne duk su ka sanya na fada, kuma sai na dauki hotunan da aka dinga zargin ba ni da lafiya. Gaskiya lafiyata kalau. Gajiyar tafiya ce kawai.