Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Rahotanni daga jihar Kano a Arewacin Najeriya, na cewa wata budurwa ta miƙa kanta ga rundunar ƴan sandan jihar biyo bayan neman da saurayin ta ɗan ƙasar Turkiyya ke yi ruwa a jallo.
Cikin wani saƙo da ɗan jarida Nazir Salisu Zango ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Laraba, ya ce “wata budurwa ta miƙa kanta ga ‘yansanda a Kano bayan da wani saurayin ta dan ƙasar Turkiyya ke neman ta ruwa a Jallo.”
Nasir Zango bai yi wani ƙarin haske kan lamarin ba, kuma zuwa yanzu babu wata hukuma data tabbatar da afkuwar lamarin.
Wannan na zuwa ne yayin da wata kotu ta aike da ɗan ƙasar Chinan nan da ake zargin ya kashe tsohuwar budurwar Ummita Kurkuku, bayan bayan kisan da ya yi mata kwanaki biyar da suka gabata.
Kungiyar Sinawa ‘yan kasuwa a Najeriya ta yi alla-wadai da kisan da ake zargin Mr Quanrong ya yi wa Ummita.
Da take mika sakon ta’aziyya ga iyayenta, kungiyar ta ce tana ba da cikakken goyon baya ga doka ta yi aikin ta.
A cikin sanarwar da ta fitar kungiyar ta ce abin da ake zargin Mr Quanrong ya aikata, abin alla-wadai ne kuma babban laifi ne da ya kamata a bar hukumomin tsaro su yi aiki don tabbatar da abin da ya faru.

Leave a Reply