Gaskiya na matsu naga nayi aure Jaruma saima Muhammad

Gaskiya na matsu naga nayi aure Jaruma saima Muhammad

Saima Muhammad jarumar wasan kwaikwayo tace ita a yanzu babban burinta shine kawai taganta da aure shine kawai muradinta a halin yanzu inda tace abin yana matukar bata sha’awa taga yara mata da kuma zawara suna aure inda tace itama dai yanzu bata da wani buri daya wuce hakan.

Saima Muhammad son kowa kin wanda ya rasa tana matukar bukatar aure dan a yanzu a shirye take ta hakura da shirin film tazo tayi aure abinda inda tace da bakinta ai darajar ya mace gidan miji duk kudin da mace zata samu bafa zataji dadin sabaatukar bata da aure.

Sai dai jama’a sun tausaya mata da fadar wannan maganar domin duk mace da akaji tana fadar haka tofa idan bata samu mijin aure ba da Matsala domin zata iya fadawa cikin wani hali domin sha’awa tafi tasiri akan mata fiye da maza.

Tace indai da akwai wanda ya shirya tofa itama ashirye take suyi aure kuma tayi alkawarin binsa sau da kafa da ladabi da kuma biyayya inda tace itama da ilmin ta daidai gwargwado ba jahila bace duk wani hakkin miji akan mace ta sani bata daga cikin matan nan masu wulakanta aure inji jarumar saima Muhammad

Kowa yaji dadi da matan kannuwood suka fara muradun suga sunyi aure su daina tabbatar a masana’antar domin suma suna su haihu suga ƴaƴansu wanda hakan ba karamin tunani sukayi na zasu taimaki kansu da kuma tarbiyyar ƴaƴansu