Gaskiya ta kara bayyana kan dalilan da fati washa ta maye gurbin Nafisa Abdullahi a film din Labarina News All

Gaskiya ta kara bayyana kan dalilan da fati washa ta maye gurbin Nafisa Abdullahi a film din Labarina

Tun San da nafisa Abdullahi tabar shirin labarina sannan kuma aka maye gurbinta da jaruma fati washa da ita wanda hakan ba karamim fusata masoya nafisa yayi ba domin ganinsu tafi kowa dacewa da wannan gurbin duba da ita aka fara ya kamata a kare da ita.

Fati washa itama dai ana ganin kamar tana da kwarewar da wasu ke ganin kamar ma tafi Nafisa Abdullahi gigewa akan harkar film sai dai kuma nafisa ta nuna mata kudi da sanin mutane tunda ta fita yawon masoya da iyayen gida a kannywood

Wannan wata hayaniya ce wacce har yanzu babu wanda yasan takamemen abinda yasa Nafisa Abdullahi tabar shirin labarina wanda a baya tace aikine yayi mata yawa shi yasa ta nemi tafice daga shirin.

A kwani nafisa ta fito ta fadi dalilin da yasa tabar shirin sai dai wasu na kallon kawai ta fadane saboda kowa yasan lokacin da sukayi fada da sarkin waka akan wani tsohon batu wanda nazirun ya fito yayi mata kaca kaca akan wannan abun

Wanda shine ake ganin babban Dalilin da yasa jarumar tayi adabo da wannan shirin mai nisan zango wanda kuma ake shirin dawowa nan kusa acikin wata me mamawa. News All