Kakakin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, Dino Melaye, yace rashin taɓuka abin a zo a gani da shugaba Buhari yayi a karagar mulki ya kashe kasuwar ɗan takarar jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, na zama shugaban ƙasa.
Buhari ya shafawa Tinubu kashin kaji
Dino Melaye, wanda ya bayyana hakan a yayin wata hira da gidan talabijin na Channels TV, yace gazawar da jam’iyyar APC tayi na samar da mafita kan halin da tattalin arziƙin ƙasar nan yake ciki ya sanya gabaɗayan ƴan takarar ta sun zama baƙar haja mai wuyar sayarwa. Jaridar The Punch ta rahoto.
Yace:
Mun yi ayyuka da dama. Mun saurari ra’ayoyin mutane, mun tattauna da mutane, sannan wannan gwamnatin ta tallata Atiku ta hanyar gazawar ta.
A yau, ɗan takara mafi wahalar tallatawa shine ɗan jam’iyyar APC, ko da a matakin kansila, ɗan majalisar jiha, ɗan majalisar wakilai, ɗan majalisar dattawa ko gwamna.
Wannan shiyasa ba zaka iya kare Bola Ahmed Tinubu ba, ba zaka iya tallata Bola Ahmed Tinubu ba, ba zaka iya kamfen ɗin zaɓen Bola Ahmed Tinubu ba, ba tare da an maka kallon sakarai ba.
Dino Melaye ya bayyana abinda ya sa Atiku ya cancanta
Melaye ya kuma ƙara da cewa:

Atiku ya shirya kan sa domin zuwan irin wannan lokacin. Ko a cikin shekara 2 da suka wuce, shine kaɗai ɗan takarar da yaje ƙaro kwalin karatun sa, ya samo digirin digir (Master’s) daga wata jami’a a Cambridge. Don haka wane ɗan takara ne yafi shiryawa a fannin ƙwarewa, kyautatawa da kuma sanin mutane?
Leave a Reply