Gwamnatin Nigeria na duba yiwuwar hana hawa babur me kafa biyu,
Gwamnatin Najeriya ta ce tana duba yuwuwar hana amfani da babura domin dakile ayyukan masu satar mutane da ‘yan ta’adda.
Ministan Shari’a kuma babban lauyan gwamnati Abubakar Malami shi ne ya sanar da haka a karshen taron majalisar tsaron kasar wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta yau Alhamis a Abuja.
miniistan ya bayyana cewa amfani da baburan na taimakawa ya ta’adda da masu satar mutane saidai bai bayyana inda dokar zatayi aiki ba da kuma sanda zasu kaddar da dokar.
Sama da shekaru Nigeria na fama matsalar satar mutane da ta’addanci musamman a fadin Arewaci kasar.
Leave a Reply