Hadiza Gabon tace tana fuskantar Barazanar zuwa kotu akan shari’ar da akeyi da ita

Idan mai karatu bai mantaba kusan watanni biyu kenan dai dawani bawan Allah yakai karar jaruma Hadiza Gabon kan cinye masa kudi kimanin naira dubu dari uku da chasa’in N390,000 kuma taki ta auresa.

Lamarin daya fusata mutumin tareda kai karar jarumar gaban alkali domin a kwatarmai hakkinsa a cewarsa.

Saidai rahotanni sun bayyana cewar a zaman kotun da akayi an bukaci lauyan mutumin su bayarda shaidunsu saidai sunkasa inda lauyan ya bayyana cewar a halin yanzu shaidun nasa basa kusa amman suna rokon kotu data basu wani lokacin domin gabatar da shaidun nasu.

Haka zalika sabida yanayi na tsaro da kasar ke ciki hakan yasa lauyan Hadiza Gabon ya roki kotu datayi watsi da wannan karar kasancewar sun kasa bada shaida kuma zuwan jarumar kotu Kusan barazana ce ga rayuwarta.

Ga video

kuci gaba da kasancewa damu a ko wane lokaci newsall.com.ng