Har yanzu akwai igiyar Aurena da Fati Muhammad cewar tsohon mijinta Sani Mai Iska

Tsohon mijin fitacciyar jarumar nan ta Kannywood wadda a shekarun baya tayi suna kamar babu gobe wato Fati Muhammad,tsohon mijin nata mai duna Sani Mai Iska ya bayyanawa BBC Hausa cewa har yanzu akwai ragowar igiyar auren su da Fati Muhammad.

Haka zalika ya bayyana cewa rabuwar tasu ta faru ne da sanin kowa domin babu wanda yake da laifi a cikin su,kawai dai tabi umarnin Mahaifiyar ta ne.

Sannan ya kara da cewa yayi mata saki biyu ne kacal,Amma kuma ita ta bayyana cewa ai uku yayi mata,bayan da aka tambayeshi shin zai iya mayar da ita gidanshi yanzu?

Sai ya bada amsar cewa besan yanzu shi wana irin ra’ayi take dashi ko kuma a wana hali take ciki yanzu.